Farfesa Yusuf M. Adam; Fir'aunonin Masar ta Dauri

Me ka ke nema?


Shafin Farko

FIR'AUNONIN MASAR TA DAURI

Takardar da za a Gabatar a Bikin Makon Hausa na Jami'ar Bayero ta Kano
Ranar, 11/9/2000


Farfesa Yusuf M. Adamu
Geography Department, Bayero University, Kano. (yusufadamu@gmail.com) Kano, Nigeria


Gabatarwa

An nemi in gabatar da makala akan Fir’aunonin Masar ta Dauri. Wannan a gaskiya ba karamin aiki ne a gare ni ba. Na farko dai wannan abu ne da ya shafi tarihin wayewar kai mafi tsawo da dadewa a duniya. Ita kuwa Masar ta Dauri gidan tarihi ce. In aka ce za yi lakca akan Masar ta dauri a kullum, za shekara guda ba a kare ba. Don haka, kada a yi tsammani zan iya yin bayani da zai zama mai gamsarwa game da Fir’aunonin Masar ta dauri, zan dai tsakura kadan daga kalilan da na sani game da taken jawabina na yau. Kafin mu shiga harkar bayani akan Fir’aunoni bari mu fara da yin sharar fage akan wasu ‘yan bayanai da suka shafi ita Daular /Daulolin Masar ta Dauri dangane da tarihinta, tsarin rayuwa da addini.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub